Ilimin Physics
Physics ilimi ne da yake nazari akan yanayi da ďabi'un abubuwa (matter). Ilimin yana lura da nazarin dangantaka tsakanin makamashi (energy) da abubuwa (matter). Masanan Physics sun karkasa shi gida biyu: Daďaďďen physics (classical physics) da kuma physics din zamani (modern physics ) Daďaďďen physics ya haďa da ilimi akan: 1. Motsi (motion) 2., Abubuwa masu ruwa-ruwa da iska (fluids) 3., Zafi (heat), 4. Sauti (sound, ) 5. Haske (light, ) 6. Wutar lantarki (electricity), and 7. Maganaďisanci (magnetism); Physics din zamani yana tattaro ilimi akan: 1 . Dangantaka ( relativity,) 2. Siffar kwayaz Zarra ( atomic structure, ) 3, Bayani kan makamashi (quantum theory, ) 4, condensed matter, 5. Ilimin nukiliya (nuclear physics, ) 6. Mafiya kankantar abubuwa (elementary particles) 7., Asali da siffar duniyoyi (cosmology) 8. Ilimin taurari (astrophysics).